Jam'iyyar PDP
An bude shafin Hukumar INEC na dora sunayen 'yan takarar gwamnoni da na majalisun jihohi amma da yiwuwar yan takara sama da 2000 ba za su kai labari a PDP da LP ba.
Tafiyar siyasar Sanata Bayero Nafada daga ƙananan hukumomi 11 na Gombe ya mara wa Pantami baya, yana mai ƙin bin tsohon jagoran zuwa APC bayan ficewarsa daga PDP.
Jam'iyyun PDP da APC sun fara dora sunayen 'yan takararsu na gwamna da majalisar jiha a shafin INEC don zaben 2027 an fadi sunayen 'yan takarar APC.
Hon. Monica Yahaya Khalto ta janye daga karar da aka shigar kan zaben fidda gwani na PDP a Gombe, ta bayyana goyon bayanta ga Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da ke neman hukumar zabe, INEC ta amince da kwamitin rikon kwarya na PDP karkashin Kabiru Turaki.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya ce rashin ingantacciyar akidar jam'iyyu ne ke haddasa yawaitar sauya sheƙar ƴan siyasa a Najeriya.
Mutane sun ce lallai Isa Pantami ya cika ‘dan siyasa da suka ji wasu kalamai da suka rika fitowa daga bakin shi a garin Balanga inda ya caccaki APC da kyau.
Baban Chinedu ya tabo Isa Ali Pantami, ya zargi malam da rashin iya mu’amala. Yusuf Haruna ya ce tsohon ministan zai iya rike Najeriya, sai dai akwai gyara a lamarin
Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta yi maraba da Kelmi Jacob Lazarus, tsohon ɗan takarar gwamnan SDP a zaɓen 2023 na Gombe, bayan ya koma cikinta.
Jam'iyyar PDP
Samu kari