Jam'iyyar PDP
Jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Gombe ta soki mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara kan wata waƙa da ta ce ta ci mutuncin Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.
Sakataren ADC na ƙaramar hukumar Gombe ya yi murabus tare da komawa PDP domin mara wa Farfesa Isa Ali Pantami baya a takarar gwamnan Gombe ta 2027.
Kotun tarayya ta yi watsi da karar PDP kan neman a kwace kujerar Anthony Attah bayan sauya sheka zuwa APC, tana mai cewa ikon yana hannun majalisar Benue.
Wasu jiga-jigan PDP biyu a jihar Gombe sun yi murabus daga jam’iyyar gabanin zaben 2027, amma ba su bayyana dalilan ficewarsu ba daga jam'iyyar mai adawa ba.
Bangaren PDP mai goyon bayan Nyesom Wike ya yi murnar fitar da sunan Sanata Sandy Onor a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027 da hukumar INEC ta yi..
PDP ta bayyana cewa tana jiran hukuncin kotu kan rikicin takarar gwamnan Gombe da ya shafi Farfesa Isa Pantami, tana mai cewa babu wani rikicin takara a jihohi.
Wasu da ake zargin 'yan daba sun kai hari kan 'yan jarida da magoya bayan PDP a Ebonyi, lamarin da ya jikkata mutane tare da jawo kira ga bincike.
Tsagin PDP na Kabiru Turaki ya ce ya miƙa wa INEC takarar Goodluck Jonathan da sauran 'yan takara, duk da rikicin amincewa da shugabancin jam'iyyar.
PDP ta kammala loda bayanan takarar Farfesa Isa Ali Pantami a shafin INEC a matsayin dan takarar gwamnan Gombe na 2027, in ji Pantamiyya Movement.
Jam'iyyar PDP
Samu kari