Jam'iyyar PDP
Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya fice daga jam’iyyar PDP a hukumance, yana cewa yana bukatar shugabanci mai maida hankali da ingantaccen aiki.
Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya musanta zargin ta’addanci, yana cewa bai da alaƙa da ‘yan ta’adda kuma bai taɓa goyon bayan aikata laifi ba.
Jam'iyyar PDP ta yi karar hukumar zabe ta kasa, INEC kan cire sunan dan takararta, Oluwole Oluyede a zaben gwamnan jihar Ekiti na 2026 da za a yi.
Tsohon sanatan Enugu ta Gabas, Gilbert Nnaji ya fice daga jam'iyyar PDP bayan kwashe shekara 27. Tsohon sanatan ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC.
Jam'iyyar PDP ta yi tsokaci kan batun sauya shekar Gwamna Caleb Mutfwang zuwa jam'iyyar APC. Ta bayyana cewa har yanzu gwamnan ne shugabanta a jihar.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi tsokaci kan batun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC. Wike ya ce akwai matsala idan ya bar PDP.
Jam’iyyar PDP a jihar Kwara ta caccaki gwamnatin AbdulRazaq kan yin shiru bayan fashewar bam a Offa, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin fargaba.
Mambobi 6 na majalisar dokokin Zamfara sun sauya sheka daga PDP zuwa APC, saboda rikice-rikicen cikin gida da dakatar da su da majalisa ta yi ba bisa ƙa'ida ba.
Shugabannin jam'iyyar PDP na duba yiwuwar komawa tsarin sulhu na Bukola Saraki domin shawo kan rikicin cikin gida da ya raba jam’iyyar gida biyu.
Jam'iyyar PDP
Samu kari