Jam'iyyar PDP
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Adamawa, Rt. Hon. Bathiya Wesley, da yan Majalisa 14 sun raba gari da PDP saboda rikicin cikin gida da ya addabi jam'iyyar.
Rahotannin da aka samu ta bayan fage sun nuna cewa Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa tare da ya majlisu sun fara shirye-shiryen tafiya jam'iyya mai mulki.
Rabiu Kwankwaso da Gwamna Seyi Makinde suna gudanar da ganawa a Ibadan wanda ake hasashen na da alaka da zaben 2027, tare da hasashe kan kulla kawancen siyasa.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya ba da tabbaci kan ci gaba da zamansa a jam'iyyar PDP mai adawa. Gwamnan ya ce zai ci gaba da adawa.
Ɗan majalisar Adamawa, Abubakar Abdullahi, ya bar PDP yau 24 ga Fabrairu, 2026. Ana sa ran wasu mambobi 5 za su bi sahun sa a zaman majalisar na ranar Laraba.
PDP ta kafa tawagar lauyoyi don ƙalubalantar nasarar APC a zaɓen ƙananan hukumomin Abuja 2026. APC ta lashe kujeru 5, yayin da PDP ta lashe Gwagwalada kawai yau.
Hukumar zabe INEC ta sanar da sakamakon zaben AMAC a Abuja, inda APC ta tabbatar da nasarar Christopher Maikalangu da kwarin gwiwar zaben shekarar 2027.
Daniel Nuhu na APC ya lashe zaɓen Kwali da ƙuri'u 17,032 a zaben ranar Asabar, 22 ga Fabrairu, 2026. Ya doke PDP a zaɓen ƙananan hukumomin Abuja.
Joshua Ishaku na APC ya lashe zaɓen Bwari da ƙuri'u 18,466 a zaben da aka gudanar ranar 21 ga Fabrairu, 2026. Ya doke ADC da ZLP bayan janyewar ɗan takarar PDP.
Jam'iyyar PDP
Samu kari