Jam'iyyar PDP
Sanata Samuel Anyanwu ya koma bakin aiki a matsayin sakataren jam'iyyar PDP na kasa. Anyanwu ya ce ya daukaka kara kan hukuncin kotu da ya sauke shi.
'Yan sanda sun mamaye hedikwatar PDP a Abuja bayan rikicin jam'iyyar PDP ya yi kamari. An samu sakatarorin jam'iyyar PDP biyu bayan hukuncin kotu.
PDP ta ce ta shirya domin kwace mulkin Najeriya a 2027. Sakataren jam'iyyar ya ce suna hade waje daya karkashin jagorancon Umar Damagun a fadin kasa baki daya.
Jam’iyyar PDP a jihar Akwa Ibom ta zabi Gwamna Umo Eno a matsayin dan takararta tilo na zaben gwamna na shekarar 2027 inda ta haramta wa sauran yan takara.
Sanata Orji Uzor Kalu da ke wakiltar Abia ta Arewa ya tarbi mutane sama da 8,000 da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC daga sauran jam'iyyun siyasa a jihar.
Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya sauke kwamishinan yaɗa labarai daga muƙaminsa, an ce hakan ba zai rasa nasaba da rashin aikin da ya kamata ba.
Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom ya ja kunnen masu kama kafa domin neman muƙami inda karyata jerin sunayen kwamishinoni da ake wallafawa a kafofin sadarwa.
Jigon jam’iyyar PDP, Emmanuel Fayose, wanda ya kasance kani ga tsohon gwamnan Ekiti Ayodele Fayose ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar gwamna.
Jam'iyyar PDP a jihar Abia, Kelvin Jumbo Onumah ya sauya sheka zuwa APC tare da dubannin magoya bayansa, ya ce zai ba da gudummuwa wajen kawo ci gaba.
Jam'iyyar PDP
Samu kari