Kamfanin wutar lantarkin Najeriya
Kamfanin samar da wutar lantarki a Abuja (AEDC) ya fara sallamar ma’aikata kusan 800 bayan watanni na sake tsari a cikin gida wanda aka yi niyyar korar 1,800.
A labarin nan, za a ji cewa kamfanin rarraba hasken wutar lantarki ya bayyana cewa za a samu matsalar daukewar wuta a wasu yakunan babban birnin tarayya.
Gwamnatin tarayya ta yi kira ga gwamnatocin jihohi da su samar da wutar lantarki a jihohinsu. Ministan makamashi ya ce gwamnatin za ta hada kai da su.
Ministan makamashin Najeriya, Bayo Adelabu ya ce Najeriya ta fara fitar da kayan sola da ta kare zuwa kasuwannin Afrika ta Yamma. Ya ce an fara fitar da su Ghana.
Masu lalata kadarorin gwamnati sun rusa hasumiyar wutar TCN a kan layin Gombe–Damaturu, wanda ya jefa Borno da Yobe cikin duhu yayin da kamfanin ke gaggawar gyara.
Kamfanin MainPower (MEDL) ya sanar da daukewar wutar lantarki na tsawon kwana 10 a Enugu daga 22 zuwa 31 Oktoba 2025, domin aikin gyara da inganta wuta.
Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa Najeriya na ci gaba da tattaunawa da kamfanin China domin gina tashar wutar lantarki ta zamani a kasar nan.
Kamfanin CCETC na kasar Sin zai gina tashar wutar lantarki da wurin masana’antu a Ogun, yayin da Gwamna Abiodun ke jawo masu zuba jari don bunkasa tattalin arziki.
Shugaban hukumar kula da wutar lantarki, NERC, Abdullahi Ramat ya bayyana cewa talakawa, makarantu da asibitoci za su amfana da rangwamen kuɗin wuta.
Kamfanin wutar lantarkin Najeriya
Samu kari