Jihar Plateau
Sojoji sun hana arangama tsakanin ƴan ƙabilar Fulani da Mwaghavul a karamar hukumar Mangu, Plateau, bayan musayar wuta kusa da kauyukan Gaude da Aloghom.
'Yan bindiga sun kashe 'yan sintiri uku 'yan uwa a Riyom, Plateau, yayin sintirin dare, lamarin da ya jawo kira ga hukumomin tsaro su dauki mataki.
Wasu mahara dauke da makamai sun kai hari kan jami’an tsaro a jihar Plateau, inda suka kashe mutum biyu tare da kwace bindigogin aikinsu a yayin harin.
'Yan bindiga sun kashe tsohon kansilan Rim Ward a Riyom da ke Plateau, yayin da wani mutum ya jikkata. Ƙungiyar Berom ta buƙaci jami'an tsaro su kamo maharan.
Tinubu ya naɗa Yakubu Jang, ɗan Jonah Jang, a matsayin Babban Mataimaki na Musamman yayin bikin cika shekaru 80 da haihuwar tsohon gwamnan Filato.
Jami’ar Jos da ke Filato ta dakatar da karatu tare da gayyatar ɗalibai taron gaggawa saboda matsalar tsaro da wasu munanan abubuwan da suka faru a jami’ar.
Mutum hudu sun bayyana yadda suka azabtar da dalibin UniJos Ibrahim Mbaye har ya mutu kan zargin satar waya. Bidiyon lamarin ya jawo fushin jama'a a Najeriya.
Matashin Jami'ar Jos Ibrahim Mbaya ya mutu bayan dukan da aka yi masa kan zargin satar iPhone, yayin da 'yan sanda suka kama mutane uku da ake zargi.
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta fara horar da ɗaliban AFMS kan sarrafa jiragen drone da fasahar zamani, yayin da 'yan Najeriya suka yaba da shirin.
Jihar Plateau
Samu kari