Jihar Plateau
Hadimin gwamnan jihar Filato ya musanta rade-radin da ake yadawa Gwamna Mutfwang ya sauka sheka daga PDP zuwa APC, ya tabbatar da cewa an fara tattaunawa.
Makiyaya sun ce an sace musu shanu 160 a kananan hukumomin Barikin Ladi da Jos ta Gabas a Filato. Sun sace an sace shanun ne bayan 'yan bindiga sun bude musu wuta.
Gwamna Caleb Mutfwang na shirin barin PDP ya koma jam'iyyar APC kafin ƙarshen Janairu 2026, duk da adawa daga wasu manyan jiga-jigan APC a jihar Plateau.
Wata kotun jiha a Plateau ta yanke wa jami'in dan sanda, Ruya Auta hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan an kama shi da laifin kashe ɗalibin UNIJOS, Rinji Bala.
Shugaban jam'iyyar APC na jihar Plateau, Rufus Bature, ya yi magana kan dalilin da ya sa ba su yi maraba da Gwamna Caleb Mutfwang ba. Ya ce ba su san niyyarsa ba.
Kungiyar Mangu Concerned Muslim Consultative Forum (MCMCF) ta karyata ikirarin Fasto Ezekiel Dachomo cewa an mayar da cocinsa da aka ƙone a Mangu zuwa masallaci.
Wasu jami'an 'yan sanda da sojoji sun ba hamata iska a jihar Filato. Rundunar 'yan sandan jihar ta bayyana cewa ta dauki mataki tare da hukunta masu laifi.
Wata kungiyar magoya bayan PDP ta shawarci Gwamna Caleb Mutfwang ya fita daga PDP zuwa APC ba tare da wani bata lokaci ba don hada kai da Bola Tinubu.
Kungiyar MURIC ta caccaki Rabaran Dachomo kan ikirarin cewa gwamnatin Musulmi da Musulmi ta haifar da “kisan gilla ga Kiristoci”, tana cewa maganarsa ba ta da tushe.
Jihar Plateau
Samu kari