Rikicin PDP
A labarin nan, za a ji cewa PDP na iya fuskantar babbar barazana yayin da gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki a Kudu maso Gabas ke barazanar ficewa.
Jami'an tsaro da aka jibge a sakatariyar PDP da ke Abuja sun fatattaki mambobin kwamitin amintattu daga dakin gudanar da taron NEC da ke a hedikwatar jam'iyyar.
'Yan sanda sun mamaye hedikwatar PDP a Abuja saboda takaddamar taron NEC, amma jam'iyyar ta tabbatar da cewa taron zai gudana kamar yadda aka tsara.
Jam'iyyar PDP a Kebbi ta shirya shiga ƙawancen 'yan adawa don kayar da APC a 2027, duk da raunin da ta samu a baya-bayan nan sakamakon sauye-sauyen sheka.
Shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP, Sanata Adolphus Wabara, ya soki matakin da mukaddashin shugaban PDP na kasa ya dauka kan dawo da Sanata Samuel Anyanwu.
Mukaddashin shugaban PDP na ƙasa, Ambasada Umar Iliya Damagum ya sanar da cewa shugabannin jam'iyyar sun amince a dawo da Samuel Anyanwu kan kujerarsa.
Shugabanni da masu faɗa a ji na jam'iyyar PDP sun kai ziyara hedikwatar hukumar zabe ta kasa watau INEC, sun tattaunawa jami'an zaɓe kan muhimmin batu.
Yan Majalisar Tarayya 2 daga jihohin Enugu da Kuros Riba sun sanar da ficewa daga jam'iyyun PDP da LP zuwa APC, sun ce ba za su iya jure rigingimun cikin gida ba.
Daga tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, har zuwa irin su Shehu Sani, Gwamna Uba Sani ya yi nasarar cika APC da kusoshin 'yan siyasar jihar.
Rikicin PDP
Samu kari