Rikicin PDP
Rikicin shugabancin da ya addabi jam'iyyar PDP ya sake daukar sabon salo bayan jam'iyyar ta dare gida biyu. An dakatar da shugaban jam'iyyar na kasa.
Jam'iyyar PDP ta dauki matakin ladabtarwa kan wasu manyan jami'anta. Jam'iyyar ta dakatar da sakatarenta na kasa tare da wasu manyan jami'ai guda uku.
Jam'iyyar PDP na ci gaba da shirye-shiryen babban taronta na kasa, sai dai akwai wadanda ake hasashen za su fafata a zaben shugaban jam'iyya na kasa a Ibadan.
Babbar Kotun Tarayya mai zama a Abuja ta umarci jam'iyyar PDP ta dakatar da shirinta na yin babban taronta a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a watan Gobe.
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya cika baki kan zaben shekarar 2026. Ya bayyana cewa babu wani dan siyasan da zai iya kayar da shi a zaben gwamna.
Jam'iyyar PDP ta rasa dukkanin 'yan majalisar wakilan da take da su a jihar Enugu. Dukkan 'yan majalisun sun sanar da sauya shekarsu zuwa APC mai mulki.
Sanatan Bayelsa ta Gabas, Benson Agadaga ya sanar da sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC a hukumance a zaman Majalisar Dattawa na yau Laraba.
Tsohon gwamna, Sule Lamido ya dauko aiki, zai yi shari'a da PDP a kotu. Sule wanda da su aka kafa jam'iyyar PDP ya na neman shugabancin jam'iyyar hamayyar.
Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta yi watsi da barazanar kai ta kara gaban kotu da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi kan kasa sayen fom din takara.
Rikicin PDP
Samu kari