Rikicin PDP
Sanata mai wakiltar Osun ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya. Olubiyi Fadeyi ya sanarda ficewarsa daga jam'iyyar PDP saboda rigingimun da suka baibaye ta.
PDP ta bayyana shirye-shiryen da take yi na dawo da Peter Obi cikin jam’iyyar, ta ce tana ganin komawarsa zai ƙara mata ƙarfi da yuwuwar nasara a zaɓen 2027.
Marcus Onobun, dan majalisar wakilai ya fice daga PDP bisa dalilin rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar. Ya ce zai sanar da jam'iyyar da zai koma nan gaba.
Daraktan yakin neman dan takarar gwamnan Edo ya yi murabus daga PDP yana mai cewa jam’iyyar ta kauce daga tsare-tsaren da aka kafata. Ya fadi abin da zai yi a gaba.
Davido ya yi wasu baituka a sabuwar waƙarsa da ke nuna Gwsmna Ademola Adeleke na shirin tattara kayansa ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.
Tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP, Dele Momodu ya sauya sheka zuwa ADC a jihar Edo. Momodu ya ce 'yan ba ni na iya sun mamaye jam'iyyar PDP.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya bayyana cewa ko kaɗan tafiyar Atiku Abubakar ba zai wa PDP illa ba, yana mai cewa jam'iyyar tana nan da ƙarfi da farin jininta.
Tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP. Atiku yana da tarihin sauya sheka a tafiyar siyasarsa.
Jam'iyyar ADC ta ce ficewar Gwamna Adeleke zuwa APC zai ba ta damar lashe zaɓen gwamnan jihar Osun na 2026, yayin da take neman jawo gwamnonin PDP biyar.
Rikicin PDP
Samu kari