Rikicin PDP
Dino Melaye da wasu manyan aminan siyasar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sun fice daga PDP sannan sun koma jam'iyyar hadaka ta ADC. Legit ta jero su.
Sanata Dino Melaye ya fice daga jam'iyyar PDP saboda rashin tasirin magance matsalolin Najeriya. Ya zargin wasu 'yan jam’iyyar da jefa ta cikin halin da ta ke ciki.
Tsohon ministan yaɗa labarai, Farfesa Jerry Gana ya bayyana cewa Peter Obi zai iya tumurmusa duk wani ɗan siyasa a Arewacin Najeriya idan ya tsaya takara a PDP.
A labarin nan, za a ji cewa tsohon mataimakin ɗan takarar gwamna a jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Kaduna ya ce akwai tarin matsaloli, saboda haka ya bar jam'iyya.
Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo ya bayyana cewa Atiku Abubakar ne jagoran siyasar Arewa duk da cewa ya fita daga PDP zuwa ADC. Ya ce PDP za ta dawo da karfinta.
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose ya bayyana cewa PDP za ta samu sakamako mafi muni a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa a 2027, za ta yi na huɗu.
PDP za ta gudanar da babban taronta a Ibadan daga 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba. Ta dauki matakin doka kan mambobin da suka sauya sheka bayan lashe zaɓe.
Farfesa Olusola-Eleka ya fice daga jam’iyyar PDP a Ekiti, yana mai zargin jam’iyyar da gaza zama cikakkiyar adawa da ingantaccen shugabanci a ƙasa.
Kungiyar iyayen PDP watau waɗanda aka kafa PDP tare da su a 1998 sun buƙaci jam'iyyar ta ɗauko wani daga Kudu ta ba shi tikitin takarar shugaban ƙasa.
Rikicin PDP
Samu kari