
Rikicin PDP







Tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar, ya roki 'yan Najeriya su tashi tsaye su kare dimokuradiyya daga barazanar dokar ta-baci a Rivers.

Tsohon ɗan takarar majalisar dokokin Kano, Hon. Adnan Mukhtar Tuduk Wada ya soki shugaban matasan PDP na ƙasa, ya ce Muhammad Kadade ya gaza wakiltar matasa.

Dakataccen gwamnan jihar Ribas, Sir Siminalayi Fubara ya tattara kayansa ya bar gidan gwamnati yayin da ake shirye-shiryen miƙa mulki ga sabon 'gwamnan riko'.

Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da cewa ta na kokarin tabbatar da mulkin danniya da murde 'yan adawa da ke fadin kasar nan.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa gwamnatin rikon kwarya a jihar Ribas jim kaɗan bayan sanar da dakatar da Gwamna Fubara da mataimakiyarsa.

Ministan Abuja, Wike ya kwace filin PDP a Abuja bisa gazawar jam’iyyar na biyan harajin filin tun 2006. FCTA ta ce ta sha jan kunne amma PDP ta ki biyan bashin.

Wasu membobin PDP sun bayyana takaicin yadda Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ke yi wa jam'iyyar karan tsaye ta hanyar goyon bayan Tinubu ya yi nasara a zaben 2027.

Mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Umar Damagum, ya bayyana rahotannin da ake yadawa masu cewa ya yi murabus, a matsayin tsantsagwaron karya.

Tsohon gwamnan Rivers kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce gwamna Siminalayi Fubara ya fadi siyasa kuma karin koma baya na nan tafe a gare shi.
Rikicin PDP
Samu kari