Jihar Oyo
Dan Majalisar Tarayya mai suna Hon. Musiliu Olaide Akinremi da ke wakiltar mazabar Ibadan ta Arewa a jihar Oyo ya rasu a yau Laraba 10 ga watan Yulin 2024.
Gwamnatin jihar Oyo ta ayyana ranar hutu domin murnar zagayowar shekarar musulunci. Gwamnatin ta ayyana ranar Litinin, 8 ga watan Yuli a matsayin ranar da ba a aiki.
Kwamishinan yan sandan Oyo ya sasanta Oba Ghandi Afolabi Olaoye da limami Yunus Tella Olushina Ayilara kan sabani da suka samu a kan zuwa aikin hajjin bana.
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar babban ɗan tsohon gwamnan jihar Oyo, Cif Kolapo Ishola mai suna Kunle Kolapo a yau Laraba 3 ga watan Yulin 2024.
An wayi gari da kulle gidajen mai a birnin Ibadan na jihar Oyo inda hakan ya jefa al'umma cikin matsala. Ma'aikata sun koka kan yadda lamarin ya kawo musu cikas.
Gamayyar malaman Musulunci a Ogbomoso da ke jihar Oyo sun kalubalanci Sheikh Taliat Yunus kan bijirewa umarnin Oba Afolabi Ghandi da ke sarautar garin.
Kwanaki bayan amincewa da bukatar masu nadin sarki, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya sanya ranar 12 ga watan Yuli domin nadin sarautar sabon sarkin Ibadan.
Mai shari’a K.B. Olawoyin na babbar kotun Oyo ya haramtawa Sarkin Ogbomoso, Oba Afolabi Ghandi Olaoye tsige babban limamin Ogbomoso, Sheik Teliat Yunus Ayilara.
Sarkin Ogbomoso da ke jihar Oyo, Oba Afolabi Ghandi ya kalubalanci limamin masallacin Juma'a kan saba ka'idar da suka yi kafin nada shi mukami a jihar.
Jihar Oyo
Samu kari