Jihar Oyo
Kungiyar NLC ta kasa ta tabbatar da rasuwar tsohon sakatarenta na kasa, Peter Ozo-Eson a asibitin UCH da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo ranar Litinin.
Fasto Elijah Ayodele ya ce Naira miliyan 150 ba za su iya sayen takalmin da yake sawa ba, yana karyata zargin karɓar kuɗin sihiri daga Bayo Adelabu.
Ministan makamashi, Bayo Adelabu, ya zargi Fasto Elijah Ayodele da neman ya karɓi N150m da kayayyaki domin ya zama gwamnan Oyo a zaben 2027 da ke tafe.
Yankin Yarbawa sun goyi bayan kafa ‘yan sandan jihohi da hukuncin kisa ga masu garkuwa, domin magance hare-haren yan bindiga da rikice-rikicen tsaro a Najeriya.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya amince a biya ma'ikata albashin watan 13. Ya ce hakan na daga cikin abin da yake yo tun bayan hawansa mulki a shekarar 2019.
Rundunar 'yan sandan Oyo ta tabbatar da sace Ibukun Otesile, diyar wanda ya kafa cocin Jesus Is King Ministries. CAN ta aika sako ga jami'an tsaro.
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da jigon jam’iyyar APC a yankin Ibadan, Hon. Wale Oriade, lokacin da yake barin ofishinsa da misalin ƙarfe 7 na yamma.
Wata kotu mai zamanta a Ibadan ta yanke wa wasu mutane biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same su da laifin kashe direban tasir a rikicin 2024.
Gwamna Makinde ya ce rikicinsa da Nyesom Wike ba na mutum 1 ba ne, rikici ne na yunkurin mayar da Najeriya karkashin jam’iyya, wanda ke barazana ga dimokuraɗiyya.
Jihar Oyo
Samu kari