
Jihar Osun







Bayan shafe shekaru ana rigima kan limancin masallaci, Kotu da ke Osun a yankin Iragbiji ta ci gaba da sauraron karar da ke tsakanin wadanda ke takarar kujerar.

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya tarbi wani jigoɓda ya dawo APC a jihar Oyo. Ya bayyana cewa jam'iyyar za ta kwato Osun, Oyo a hannun PDP.

Jami’ar OAU ta shiga alhini bayan Farfesa Jimoh Olanipekun ya yanke jiki ya fadi ana taro. An gaggauta kai shi asibiti, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.

Gwamna Adeleke ya gana da Bisi Akande kan rikicin kananan hukumomi, yana mai cewa gwamnatinsa na bin doka. Akande ya bukaci zaman lafiya da bin doka a Osun.

Bayan gargadin gwamnatin Bola Tinubu kan sake zaben kananan hukumomi, Gwamna Ademola Adeleke ya dage cewa za a gudanar da zaben a Osun a gobe Asabar.

Tinubu ya amince da sabbin jami’o’i a Ekiti da Osun don inganta noma, fasaha da muhalli, tare da bunkasa tattalin arziki da kirkire-kirkire a Najeriya.

Bayan hukuncin kotu da kuma rigimar da aka samu kan ikon kananan hukumomi, jam’iyyar APC ta janye daga zaben a Osun da aka shirya ranar 22 ga Fabrairun 2025.

Jam'iyyar PDP ta zargi sufetan ƴan sandan Najeriya ta hannu a yunkurin APC na kashe gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun, ta ce duk abin da ke faruwa makirci ne.

Duk da rigimar da ta barke da aka rasa rayuka a Osun kan ikon ƙananan hukumomi, shugabannin APC na yankuna 14 da kansiloli a Osun sun koma ofisoshinsu.
Jihar Osun
Samu kari