Zaben Ondo
A ranar Asabar, mazauna jihar Ondo za su sake zabar gwamna wanda zai yi wa’adin shekara hudu a kan mulki, kuma akwai laifuffuka da ya dace yan siyasa su lura da su.
Sa'o'i 24 gabanin fafata zabe, kotun ɗaukaka kara ta kori ɗan takarar gwamna na jam'iyyar LP, Chief Olusola Ebiseni, ts yu fatali da hukuncin babbar kotun tarayya.
Jam'iyyar PDP ta yi zargin maguɗi a zaben Ondo. PDP ta ce APC ta shirya murɗe zaben Ondo. Kashim Shettima zai dura Ondo yakin neman zaben gwamna.
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya fadi gwagwarmayar takara da yayi a zaben 1999. Obasanjo ya yi fatan alheri ga dan takarar APC a zaɓen Ondo.
Kayan zabe masu muhimmanci sun isa Akure a jihar Ondo yayin da jam’iyyu ke shirin tunkarar zabe mai zuwa da za a gudanar a ranar 16 Nuwamba, 2024.
Kungiyar matasan APC a jihar Ondo (Ondo Patriots) ta yi watsi dan takararta kuma Gwamna Lucky Aiyedatiwa a zaben da za a gudanar inda ta bi dan SDP.
IGP Kayode Egbetokun ya sanar da tura jami'ai 22,239 zuwa Ondo don tabbatar da tsaro a zaben gwamna mai zuwa. Ya kuma zargi jam'iyyun siyasa da haddasa husuma.
Babbar Kotun jihar Ondo ta yi fatali da korafin masu kalubalantar takarar Olugbenga Edema a zaben gwamnan Ondo kan zargin cewa ba dan NNPP ba ne.
Dan takarar jam'iyyar NNPP a zaben jihar Ondo, Gbenga Edema yana cigaba da jiran tsammani duk da daura kwanaki 11 a gudanar da zabe duba da korafi da ke kansa.
Zaben Ondo
Samu kari