
Zaben Ondo







Jam'iyya mai mulki ta APC ta sake samun nasara a zaben gwamna a Najeriya, inda dan takararta, Lukcy Aiyedatiwa ya koma kujerar da ya ke kai ta gwamnan jihar Ondo.

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya taya Gwamna Lucky Aiyedatiwa murnar lashe zaben gwamnan jihar Ondo wanda aka yi a jiya Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024.

Shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Ganduje ya taya Gwamna Lucky Aiyedatiwa murnar lashe zaben Ondo inda ya ce saura su kwace jihohin Osun da Oyo.

A ranar Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024 da muke ciki aka fara kada kuri'a a zaben jihar Ondo inda za a fafata tsakanin APC da PDP da LP da NNPP da sauransu.

Rahoton Yiaga Africa ya nuna yadda APC da PDP saka saye kuri'u a zaɓen Ondo. Talakawa sun sayar da kuri'unsu a zaben a kan N5,000 zuwa N10,000 a zaben Ondo.

Yayin da ake cigaba da zaben jihar Ondo, dan takarar PDP, Ajayi Agboola ya nuna damuwa kan yadda aka yi ta samun korafe-korafe kan zaben da aka gudanar.

Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Ondo na kan gaba a sakamakon zaben gwamnan Ondo da aka sanar na kananan hukumomi 15. PDP na biye da ita a can baya.

Dan takarar gwamnan jam'iyyar APC na jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya shiga gaban na PDP bayan sanar da sakamakon zabe daga kananan hukumomi 15 na jihar.

A ranar Asabar, 16 ga watan Satumba ne hukumar INEC ta gudanar da zaben jihar Ondo. A halin da ake ciki, INEC ta fara sanar da sakamakon zaben daga kananan hukumomi.
Zaben Ondo
Samu kari