
Zaben Ondo







Gwamnan jihar Ondo, Hon. Lucky Aiyedatiwa ya sanar da sa dokar hana fita ta tsawon awanni tun daga safiya har dare a garin Owo, hedkwstar ƙaramar hunumar Owo.

Wata kotun tarayya ta kori karar da PDP ta shigar da dan takarar APC kuma gwamnan jihar Ondo. Kotun ta ce PDP ta yi jinkirin shigar da karar inda ta saba dokar zabe.

Wasu daga cikin 'yan takarar da suka fafata a zaben gwamnan jihar Ondo, sun nuna goyon bayansi ga Gwamna Lucky Aiyedatiwa. Sun bayyana cewa sun amince da nasararsa.

Jam'iyar PDP ta shigar da karar Abdullahi Ganduje wajen Bola Tinubu kan maganar kwace mulki a Oyo da Osun. Ta ce kalaman za su iya tayar da hankali

Shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana kokarin da suka yi wurin tabbatar da nasarar jam'iyyar APC a jihar ba tare da katsalandan ba daga wasu bangare.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ba da takardar shaidar lashe zabe ga zababben gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa da mataimakinsa.

Wasu yan APC sun yi haɗari yayin yakin neman zabe a jihar Ondo. Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya ziyarci waɗanda suka yi hadarin suna kwance a asibiti a Ondo.

Jam'iyyar PDP ta sha kashi a hannun APC a zaben gwamnan jihar Ondo da aka kammala ranar Asabar, wannan ne rashin nasara mafi muni da ta yi tun 1999.

Jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Ondo ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan jihar wanda APC ta lashe. PDP ta ce za ta garzaya zuwa kotu domin kalubalantarsa.
Zaben Ondo
Samu kari