
Ogun







Atiku Abubakar ya gana da tsohon Shugaban Kasa Obasanjo a Abeokuta. Ana hasashen tattaunawar ta shafi shirye-shiryen tunkarar zaben 2027 tare da sauran ‘yan hamayya.

Gwamnan jihar Ogun ya yi jimamin rasuwar sarkin, Iperu-Remo, Oba Adeleke Adelekan Idowu-Basibo, ya ce wannan rashi ne da zai wahala a iya maye gurbinsa.

Mai martaba sarki na masarautar Orile Ifo, Oba Abdulsemiu Ogunjobi ya tsinci kansa a gidan gyaran hali bayan gaza cika sharuddan belin da aka ba shi a Ogun.

Rundunar ƴan sandan jihar Ogun ta gurfanar da wani dattijo a gabam kuliya kan tuhumar haɗin kai, cin zarafin wani bawan Allah, kotu ta ɗage zaman.

Bayan zargin cin zarafi da wani basarake ya yi, Gwamnatin jihar Ogun ta dakatar da Oba Abdulsemiu Ogunjobi na Orile Ifo na tsawon watanni shida daga sarauta.

Sallar jana'iza ta Musulmi da aka ga Sanata Otunba Gbenga Daniel ya yi ta haifar da cece kuce a jihar Ogun, wani makusancin tsohon gwamnan ya yi bayani.

Gwamnatin Ogun ta fara bincike kan bidiyon da ya nuna Oba Ogunjobi yana cin zarafin Cif Arinola, yana la’antar shi da barazanar amfani da ‘yan sanda kansa.

'Yan sanda sun kama barawon da ake zargi da sace kayan masallaci da suka kai N520,000. Barawon ya sace fankoki da tagoggin masallacin ya sayar da su.

Babbar kotun jihar Ogun ta soke naɗin basaraken Ilawo, ta ce Gwamna Dapo Abiodun ya rainata da ya ci gaba da harkokin naɗa sarkin duk da an shigar da ƙara.
Ogun
Samu kari