Ogun
’Yan sanda sun cafke Gandonu Lowe a Yewa ta Kudu bayan kama shi yana yunkurin tserewa da gawar matarsa da ya nade cikin buhu ya ɗaure a babur dinsa.
Yan kasuwa da masu ruwa da tsaki a harkokin noma sun jinjina wa gwamnatin tarayya bisa yadda tsadar kayan abinci ke kara a jihohi iirinsu Kwara, Ogun da Oyo.
Majalisar Wakilai ta fara tattake wuri kan kudirin kirkiro jihar Ijebu daga cikin Ogun, an mika shi ga kwamitin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya don nazari.
An tabbatar da cewa jami'ar a hukumar LASRRA, Hajiya Serifat Olubukola Talabi, ta rasu kwana hudu kafin ritayarta da kuma zagayowar ranar haihuwarta.
Bayan mutuwar marigayi Sarkin Ijebu da aka birne bisa tsarin Musulunci, mutuwarsa ta haifar da rikici tsakanin masu ra’ayin gargajiya da na addini.
Kamfanin CCETC na kasar Sin zai gina tashar wutar lantarki da wurin masana’antu a Ogun, yayin da Gwamna Abiodun ke jawo masu zuba jari don bunkasa tattalin arziki.
Kwamishinan ‘yan sanda a Ondo, Adebowale Lawal, ya ce an samu bindigogi, harsasai da magungunan tsafi daga hannun wadanda ake zargi da shirin kashe Sarki.
Ana zargin tirelar simintin Dangote ta haddasa mummunan hatsari a jihar Ogun inda mutum biyar suka mutu bayan ta rasa birki ta buge adaidaita sahu a Papalanto–Ilaro.
Rahotanni daga jihar Ogun sun bayyana cewa wata tanka da ta dauko man fetur ta fashe a kan totin Abeokuta zuwa Sagamu, ana fargabar mutane da dama sun mutu.
Ogun
Samu kari