Sarkin Kano
A yau Asabar 20 ga watan Yulin 2024 aka gayyaci Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero zuwa addu'a ta musamman da aka shirya a gidan Khalifa Isyaka Rabiu a jihar.
Gwamnati ta ce Sarkin Gaya ne kadai ya rungumi kaddara lokacin da aka rushe masarautu a Kano. Kalaman Sarkin Gaya da suka sa ya koma karaga bayan tsige Sarakuna.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya miƙawa sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Abdulƙadir takardar naɗinsa bayan dawo da shi kan karagar mulki ranar Laraba.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yabawa Gwamna Abba Kabir kan matakin raba takin zamani ga al'umma inda ya ce hakan zai taimaka wurin samar da abinci.
Sabon sarkin Karaye, Muhammad Maharaz ya ziyarci fadar sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi na biyu kwana daya da nada shi a matsayin sabon sarki.
Jigon PDP, Abdul-azizi Na'ibi Abubakar ya magantu kan matakan da Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ke dauka inda ya ce ya dauki matakai da dama amma yanzu yana nadama.
Bayan zartar da kudurin dokar kirkirar sarakunan gargajiya masu daraja lamba biyu a Kano, ga wasu muhimman abubuwa 3 da ya kamata ku sani game da masarautun.
Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano, Lawal Hussain ya bayyana cewa a yanzu haka Aminu Ado Bayero bai cikin sarakunan jihar a lissafin hukuma.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada sababbin sarakuna a masarautun da ya kirkiro guda uku a jihar. Masarautun sun hada da Karaye, Rano da Gaya.
Sarkin Kano
Samu kari