Sarkin Kano
Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi ya halarci gasar wasan polo da bankin Access ya shirya na 2025 a ƙasar Ingila, ya haɗu da Thomas Tuchel.
Ana zargin Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da bayar da umarnin korar wasu masoyan Aminu Ado Bayero daga fadar Sarki saboda rashin biyayya a fada.
Wata kungiya ta roki kotun kolin Najeriya ta gaggauta ya yanke hukunci kan rigimar masarautar Kano tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.
Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana cewa ba haka kurum magoya bayansa suka tada rigima a fadar Kofar Kudu ba, tilasta masu aka yi su kare kansu.
Daya daga cikin bayi a fadar Sarki Sanusi II, Usman Sallama Dako ya koka kan yadda iyalansa ke fuskantar tozarci, yana zargin Sarki da rashin adalci da tausayi.
Kungiyoyin fararen hula a Kano sun nuna ɓacin ransu kan farmakin da magoya bayan Aminu Ado Bayero suka kai fadar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.
Bayan rigima ta barke tsakanin magoya bayan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero, basaraken ya bar Najeriya zuwa Afrika ta Kudu domin halartar taro.
A labarin nan, za a ji cewa rundunar yan sandan Kano ta fara samun nasara a kan wasu daga cikin mutanen da ake zargin suna da hannu a wajen rikicin Kofar Kudu.
Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta nuna danuwa kan yadda aka yi fada a fadar Sarki Muhammadu Sanusi duk da akwai jami'an tsaro.
Sarkin Kano
Samu kari