Nyesom Wike
MURIC ta bukaci Nyesom Wike ya bayyana dalilin dakatar da Injiniya Shehu Hadi, tana mai cewa rashin bayani na nuna rashin bin ka'ida da rashin adalci wajen korar.
Likitocin ARD-FCTA ta gargadi Wike kan yajin aiki mafi muni idan ba a biya bukatunsu ba cikin kwanaki 14, ciki har da albashi, kudin kayan aiki, da gyaran dokoki.
Wike ya shirya karbar makudan kudi daga mamallaka filaye a Abuja. Za a tatso biliyoyin Naira daga masu matsala da takardar mallakar kadara a Maitama.
Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jajanta wa Bola Tinubu kan turmutsitsin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a jihohin Najeriya a wannan mako.
Shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Tajudden Abbas ya ƙaryata labarin da ake yaɗawa game da kwace masa fili a Abuja inda ya ce ko sisin kwabo ba a binsa.
Bayan kwace filayen Muhammadu Buhari da yan siyasa, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ba da wa'adin mako biyu ga wadanda abin ya shafa da su biya kudin da ake bukata.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya mayar da martani ta bakin kakakinsa, Garba Shehu inda ya ce ba mai gidan nasa ba ne ya siya filin da hannunsa.
Minista Wike ya kwace filaye 762 a Maitama, Abuja, ciki har da na Buhari, bisa rashin biyan haraji; masu filaye 614 na da wa'adin makonni biyu su biya.
Jami'an rusau a babban birnin tarayya Abuja sun gamu da sojoji.An yi zargin ma'aikatan Wike na shirin rushe ginin babban soja a lokacin da jami'an su ka isa wajen.
Nyesom Wike
Samu kari