Labaran NNPC
Matatar Dangote ta sanar da daina sayar da man fetur da Naira bayan korar wasu ma'aikata. PENGASSAN ta ce za ta yi bore domin adawa da korar ma'akatan.
NNPC ya samu N318.05bn daga Janairu zuwa Agusta, 2025 don nemo mai a yankunan Sokoto, Neja da wasu hudu, wanda ya zama 30% na ribar PSC daga rabon FAAC.
A labarin nan, za a ji cewa 'yan kasuwar mai sun harzuka bayan sun ji labarin cewa gwamnatin tarayya na shirin sayar da kadarorin hadin gwiwa da ta mallaka a NNPCL.
Kamfanin NNPC ya samu ₦1.06trn daga ribar PSC tsakanin Janairu–Agusta 2025 amma bai tura kudin rabosan ga FAAC ba, abin da ya jawo tambayoyi kan kudaden shiga.
Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa yan kasuwa da ke shigo da man fetur daga kasashen waje sun nemi ya saka musu tallafin man fetur na Naira tiriliyan 1.5.
Tsohon shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari ya yi magana bayan gayyatar da EFCC ta masa domin amsa tambayoyi kan badakalar kudin gwamnatin Najeriya.
Matatar Dangote ta tabbatar da kammala shirye shiryen raba mai kyauta a jihohin Najeriya. Za a fara da Abuja da wasu jihohi 10 kafin shirin ya fadada daga baya.
Wata kotun Amurka ta samu tsohon manajan NNPCL, Paulinus Okoronkwo, da laifin rashawar $2.1m (₦3.1bn). Yana iya fuskantar ɗaurin shekaru 25 a kurkuku.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta titsiye tsohon shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Mele Kyari, kan zargin karkatar da kudade masu yawa.
Labaran NNPC
Samu kari