Matasan Najeriya
Wasu matasa sun kashe rayuka da dama a jihar Edo kan zargin garkuwa da mutane. Matasan sun kona ofihin yan sanda da kona shaguna da gidajen al'umma.
Shugaban Majalisar Dattawa, Mista Godswill Akpabio ya ba yan Najeriya shawara da cewa duk inda suka ga abincin kyauta su ci saboda halin kunci da ake ciki.
A ranar Juma'ar nan gwamna Abba Kabir Yusuf ya shige gaba zuwa makarantar 'Governors' College' domin kai wasu muhimman kaya ciki har da kujerun zama 1000 ga dalibai.
Isabel Anani, 'yar shekara 16 mai fafutukar daidaiton jinsi ta zama shugabar majalisar wakilai na wucin gadi yayin da ake bikin 'ranar 'ya'ya mata ta duniya.'
An kama matasa uku da suka kashe mai gidansu a Kano ta hanyar caccaka masa wuka bayan sun saka masa guba a abinci. Matasan sun kona gawar mai gidansu.
Tsohon gwamnan jihar Rivers kuma Minista a gwamnatin Muhammadu Buhari, Rotimi Amaechi ya nuna damuwa kan halin aka jefa yan Najeriya a ciki na tsadar rayuwa.
Gwamnatin tarayya karkashin shirin shugaban nasa na P-CNG, ta kaddamar da shafin da matasa za su nemi tallafin Keke-Napep 2,000 da za ta rabawa matasa.
Rabi'u Kwankwaso ya ce zai tabbatar da kowane talaka ya samu rayuwa mai inganci a Najeriya. Ya ce za su samar da tauraro a kowane gidan talakan Najeriya.
Gwamnatin ƙasar Rasha ta musanta zargin hannu a zanga-zangar 1 ga watan Oktoba, 2024 da aka yi a Najeriya, ta ce ƙasashen yamma ne ke naman haɗa faɗa.
Matasan Najeriya
Samu kari