Matasan Najeriya
Gamayyar malaman addinin Musulunci a jihar Ogun sun yi Allah wadai da shirin gudanar da zanga-zanga a fadin Najeriya inda suka shawarci matasa kan haka.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce marasa kishin ƙasa ne ke rura wutar shirya wannan zanga-zangar da za a yi, ya ce duka suna da fasfon zama a ƙetare.
Rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta gurfanar da wani matashi mai shekaru 19 kan zarginsa da ɓalle Masallaci tare da sace wayar zamani ta N100,000 ta wata mata.
Rundunar 'yan sanda ta tura jami'anta akalla 4,200 birnin Tarayya Abuja domin dakile miyagu da za su shiga zanga-zanga da matasa ke shirin yi a Najeriya.
Bayan amincewa da kudurin dokar sabon mafi karancin albashi da majalisa ta yi, an rika samun rade-radin cewa Shugaba Bola Tinubu na iya karawa 'yan NYSC alawus.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ya taɓa fita zanga-zanga a ƙasar nan amma ta lumana. Ya ce ba zai lamunci ɓarnatar da dukiya ko rayukan jama'a ba.
Daniel Bwala ya caccaki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubukar bisa nuna goyon baya ga zanga zangar da matasan Najeriya ke shirin yi.
Kungiyar matasan Najeriya ta yi tattaunawar gaggawa da mambobinta daga jihohin kasar nan 36 a kan batun zanga-zanga da ake shirin gudanarwa daga 1 Agusta, 2024.
Cocin ECWA a jihar Filato ya bukaci matasa da ke cocin su nisanci fita zanga zangar tsadar rayuwa da ake shirin gudanarwa saboda kaucewa ta da tarzoma a kasa.
Matasan Najeriya
Samu kari