Matasan Najeriya
Jam'iyyar PDP ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jayne tsare tsaren da ya kawo domin kawo saukin rayuwa ga yan Najeriya da suka jawo zanga zanga.
Rahotannis sun nuna cewa aƙalla mutane biyar ne suka samu raunuka yayin da ƴan sanda suka sa ƙargi wajen tarwatsa masu zanga zanga a birnin tarayya Abuja.
Wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta ya nuna lokacin da Kiristoci ke ba Musulmai kariya a lokacin da suke yin sallar Juma'a ana tsaka da zanga-zanga.
Gwamnatin Kano ta ce ta sassauta dokar hana fita ta awanni 24 da ta sanya a fadin jihar a jiya Alhamis domin ba al'umma damar zuwa masallacin Juma'a.
Gwamnatin Borno da hukumomin tsaro sun sanar da sassauta dokar zaman gidan da aka sanya daga karfe 12:00 zuwa 3:00 na rana domin mutane su je masallaci.
Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, Olumuyiwa Adejobi ya fitar da hotuna da kuma bidiyo na yadda masu zanga-zanga ke satar dukiyar jama'a a Kano a ranar Alhamis.
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban karamar hukumar Karu da ke jihar Nasarawa ya sanya dokar hana fita ta awanni 12 bayan bullar rahoton tashin hankula.
Jami'an ƴan sanda sun tarwatsa masu zanga zanga da suka sake fitowa a babban shataletalen Beger da ke birnin tarayya Abuja, sun harba barkonon tsohuwa.
Rundunar Kano sun bayyana nasarar cafke karin matasan da ake zargi da fasa wuraren ajiyar kayan abincin jama'a tare da wasosonsu a ranar Alhamis.
Matasan Najeriya
Samu kari