Matasan Najeriya
Gwamnatin Kano ta ce ta sassauta dokar hana fita ta awa 24 da ta sanya a fadin jihar. Gwamnatin jihar ya ce yanzu dokar za ta fara aiki 6 na safe zuwa 6 na yamma.
Masu shirya zanga-zangar da ake yi a jihar Legas sun sanar da tafiya hutun kwana ɗaya tal domin duba abubuwaɓ da suka faru da ɗaukarmataki na gaba.
Rundunar 'yan sandan Kano ta kama mutanen bisa zargin sata, lalata kadarorin jama'a da na gwamnati, tayar da hankula da gudanar da taro ba bisa ka'ida ba.
Wani jigo a jam'iyyar APC ya yi kira ga matasan Najeriya kan cigaba da ba Bola Tinubu goyon baya. Olamide Lawal ya ce zanga zanga ba mafita ba ce ga kasa baki daya.
Gwamna Francis Nwifuru ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta rabawa matasa 1,300 tallafin kudi domim su dogara da kansu saboda ƙin shiga zanga zanga.
Rundunar yan sanda ta dauki matakin doka kan masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa 26 a Kaduna, alkali ya tura su gidan gyaran hali, ta kama wasu 39.
Iyalan wani matashi dan shekara 25 mai suna Bashir Muhammad sun nemi gwamnati da ta yi masu adalci tare da bin kadin jinin dan uwansu da jami'an tsaro suka kashe.
Kungiyar dattawan Arewa ta yi magana kan jawabin da Bola Ahmed Tinubu ya yi a ranar Lahadi kan zanga zanga da aka fara a Najeriya, ta ce bai ba Arewa muhimmanci ba
Jigon jam'iyyar APC ya shawarci Bola Tinubu kan abin da ya kamata ya yi kan masu daga tutucin Rasha yayin da ake cigaba da zanga-zangar tsadar rayuwa a kasar.
Matasan Najeriya
Samu kari