Matasan Najeriya
Ministan kasafi da tsare-tsare, Alhaji Atiku Bagudu ya bayyana cewa zanga zangar da ƴan Najeriya suka ta jawo hankalin gwamnati da rika sauraron koken jama'a.
Mata a jihar Ondo sun ce halin kuncin da su ke ciki ya kai makura, domin ba sa iya ciyar da kawunansu ballantana yaransu, ko kuma biya masu kudin makaranta.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta ce kar dalibai su ji tsoron shirinta na gwajin kwaya idan za a fara sabon zangon karatu domin taimaka masu.
Matasan Najeriya a kafar X sun yi rubdugu ga Reno Omokri kan kokarinsa na kare gwamnatin tarayya kan sayen sabon jirgi ga shugaban kasa Bola Tinubu.
Gwamnatin Najeriya ta ce ana kashe Naira 120 domin samar da kilowatt 1 na wutar lantarki a kowacce awa. Ta kuma fadi shirinta na kara kudin wutar.
Kungiyar matasa masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku sun ce babu wani mahaluki da zai iya dakatar da Atiku a zaben shugaban kasa na 2027.
Shugaban matasan APC, Dayo Isael ya bayyana shirin da suka yi na taron matasa na kasa a watan Satumba mai kamawa. Bola Tinubu da Kashim Shettima za su haralci taron.
Tsohon shugaban kasa,Cif Olusegun Obasanjo ya ce ba ya goyon bayan ware wata kabila ko korarsu daga Najeriya, domin kasar ta dukkanin mazauna cikinta ne.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu ne ya yanke shawarar saka Naira biliyan 50 cikin asusun ba da lamun ilimi na Najeriya (NELFUND).
Matasan Najeriya
Samu kari