Jami'o'in Najeriya
Gwamnan jihar Neja ya yafewa daliban jami'ar Abdulkadir Kure da suka fara karatu kudin makaranta na zangon 2024|2025. Ya ba dukkan daliban kyautar N100,000.
Kungiyar malaman jami'a ta ASUU ta sanar da janye yajin aikin mako biyu da ta shiga domin gargadin gwamnati. Ta ba gwamnatin Tinubu wata daya ta biya bukatunta.
Wani kusa a jam'iyyar APC kuma tsohon dan majalisar wakilai, Farfesa Haruna Yerima ya shawarci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan yajin aikin ASUU.
Babbar Kotun Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan mutane 2 da aka kama da laifin kai hari tare da kashe malamin jami'ar Yusuf Maitama Sule, Kano.
Gwamnatin Tarayya ta karyata jita-jitar da ke yawo cewa JAMB ba zai sake zama wajibi wajen samun gurbin shiga jami’o’i da sauran makarantun gaba da sakandire.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta nuna rashin jin dadinta kan yajin aikin kungiyar ASUU. Ta bukaci shugabannin jami'o'i su rike albashin mambobin kungiyar.
Kungiyar malaman jami'o'i, ASUU ta sanar da shiga yajin aiki na makonni biyu a duk jami’o’in gwamnati daga Litinin, 13 ga Oktobar 2025 yayin taro a Abuja.
Bayan soke digiri dan Kotono a wasu jami'o'in Benin da sun fito da dabarar shiga shirin NYSC bayan gwamnatin Najeriya ta soke jami'o'in da suke karatu a ketare.
Kungiyoyin Ma'aikatan Jami'o'i da Kwalejojin Ilimi na Tarayya aun fara zanga zangar lumana kan rashin cika alakwarin gwamnatin Najeriya tun 2009.
Jami'o'in Najeriya
Samu kari