Jami'o'in Najeriya
Malamin adinin musulunci a Najeriya, Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo ya samu karin matsayi zuwa Farfesa daga jami'ar Bayero ta Kano a yau Juma'a.
Rundunar ƴan sanda ta tabatar da nutuwar ɗaliban Jami'ar OOU 3 a wani mummunan hatsarin mota da ya afku jiya Juma'a, wasu mutum 2 na kwance a asibiti.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu da ake zargin masu kwacen mota ne sun bindige lakcara, Dr. Fabian Osita da ke koyarwa a Jami'ar Nnamdi Azikiwe a Anambra.
Gwamnatin tarayya ta sauya sunan Jami’ar Abuja zuwa Jami’ar Yakubu Gowon don girmama tsohon shugaban kasa. Kudurin yana jiran amincewar majalisar tarayya.
Ice Prince ya bayyana wahalhalunsa a matsayin maraya, ya gaza shiga jami’a saboda N20,000, amma ya ce nasararsa hujja ce cewa komai zai yiwu a rayuwa.
Jami'ar Sule Lamido ta amince da nazarin wakokin Nura M Inuwa. Mawakin ya bayyana wakokin da za a bincika, ciki har da "Hindu" da "Bakin Alkami."
Rahoto ya nuna cewa majalisar tarayya ta amince da kudurin da aka gabatar gabanta na kafa jami'ar ma'adanai ta tarayya a garin Jos, babban birnin jihar Filato.
Kungiyar ASUU reshen jami'ar LASU ta fara yajin aiki saboda rashin biyan karin albashi da gwamnati ta gaza aiwatarwa tun Janairu 2023. An ba dalibai hakuri.
Malamin jami'ar Uyo, Inih Ebong ya samu nasara a kotu bayan fafutkar shekaru 22 yana zuwa kotuna. Kotu ta umarci a biya shi hakkokinsa na shekarun.
Jami'o'in Najeriya
Samu kari