Majalisar dattawan Najeriya
Sanatan Sokoto ta Gabas, Ibrahim Lamido, ya bayyana dalilin da ya sanya ya hakura da sake neman komawa majalisa yayin da ya gaza samun tikitin takarar gwamna.
Tsohon gwamnan jihar Gombe, Danjuma Goje ya rasa tikitin APC na neman komawa Majalisar dattawa karo na biyar a zaben fitar da gwanin da aka gudanar.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya samu nasarar lashe tikitin APC domin neman tazarce a mazabar Kano ta Arewa a zaben 2027.
Sanata Akpabio, Barau Jibrin, gwamnoni bakwai da wasu tsofaffin gwamnoni sun shiga zaben fitar da gwani na kujerun Sanata a APC gabanin zaben 2027.
Jam’iyyar APC ta fitar da cikakken jerin sunayen mutum 47 da aka hana shiga takarar Sanata a zaben fitar da gwani na 2027, ciki har da Ben Murray-Bruce.
A labarin n an, za a ji cewa gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da wasu manyan APC sun zauna domin kashe rikicin Hon Rurum da Sanata Kawu Sumaila.
Sanata mai wakiltar Kebbi ta Kudu a majalisar dattawa, Garba Maidoki, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC. Ya kafa hujja da rikicin cikin gida a jam'iyyar.
Sanata Ahmed Lawan ya sake sayan fom din takara domin tsayawa a zaben shekarar 2027 duk da cewa shi ne sanatan ya fi kowane dan majalisar tarayya dadewa a Najeriya.
Sanatan Borno ta Tsakiya, Sanata Kaka Shehu Lawan, ya rabawa shugabannin APC na mazabarsa N135.65m domin tallafa musu bikin Babbar Sallah mai zuwa.
Majalisar dattawan Najeriya
Samu kari