
Albashin ma'aikatan najeriya







Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da mukaddashin shugaban ma'aikatan jihar, Salisu Mustapha kan zargin cire kudi daga albashin ma'aikata ba bisa ka’ida ba.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake yankewa wasu ma'aikata albashinsu. Ya kafa kwamitin bincike kan lamarin.

Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya umarci shugabannin kananan hukumomi su fara biyan mafi karancin albashin N85,000 domin cika ka'idar aiki.

Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa ta na sane da ma'aikatan kasar nan, kuma a dauke da sauye-sauye da za su kawo canji a rayuwarsu a gaba kadan.

Gwamnatin Dauda Lawal Dare ta bayyana cewa an gudanar da bincike don tantance ma'aikatan jihar a kokarin fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin N70,000.

Gwamnonin jihohi 36 za su kashe kudi har N3.87tn kan albashin ma'aikata a shekarar 2025. Hakan na zuwa ne bayan karin albashin N70,000 da aka yi.

Malaman Ebonyi sun shiga yajin aikin sai baba-ta-gani bayan wasu shugabannin kananan hukumomi sun gaza biyan albashin watanni uku na malaman firamare.

Gwamnatin jihar Sokoto ta yi magana kan lokacin fara biyan sabon mafi karancin albashi. Ta ce za ta fara biyan ma'aikatan sabon albashin daga watan Janairun 2025.

Gwamnatin jihar Oyo karkashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde ta cika alkawarin da ta daukarwa ma'aikata inda ta fara biyan sabon mafi karancin albashi.
Albashin ma'aikatan najeriya
Samu kari