
Yaran masu kudi







Hamisu Haruna ya auri ‘yar shekara 14 amma tun kafin ya shiga daki ta kusa kashe shi. Ango mijin amarya ya ce yaudarar budurwar aka yi, tsohon saurayi ya ba ta guba.

Wani saurayi ya siya wa fitacciyar 'yar TikTok a Arewa, Maryam Sa'idu gida na N55m, ya ce ta daina zama a otel. Maryam ta ce ba za ta yi aure ba sai Tinubu ya sauka.

Yunkurin yin tafiye-tafiye ba tare da biza ba a Afirka na karuwa, inda a baya-bayan nan kasashe kamar Rwanda da Kenya suka bude iyakokinsu ga daukacin 'yan Afirka.

Darajar Naira ta kai N1,670 kan dalar Amurka a kasuwar bayan fage, inda masu canji ke danganta hakan da ƙarancin daloli da hauhawar bukatarta a kasuwar.

Bincike ya biyo kan tsohuwar matar babban sarki Ooni na Ife, Naomi Shikemi kan mutuwar yara 32 a makarantar Musulunci a Oyo yayin wani taron nishadi.

Ice Prince ya bayyana wahalhalunsa a matsayin maraya, ya gaza shiga jami’a saboda N20,000, amma ya ce nasararsa hujja ce cewa komai zai yiwu a rayuwa.

Ibrahim Mukhtar ba zai hakura da ruguza gininsa da jami’an KNUPDA suka yi a jihar Kano ba Yake cewa sun wayi gari ne kurum, sai suka ji labarin an kai ginin kasa.

Mai kudin duniya watau Elon Musk ya na da dukiyar ta kusa kai Dala biliyan 450. A zamanin nan, ba a taba samun labarin mutumin da ya tara Dala biliyan 400 ba.

Bankuna a jihar Nasarawa sun rage cire kudi, wanda ya jawo masu POS ke caji mai tsada. Jama'a sun fara korafi yayin da suke fuskantar wahala saboda karancin kudi.
Yaran masu kudi
Samu kari