Malaman Izala da darika
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba limamin Ibadan, Sheikh Abdul-Ganiyy Agbotomokekere kyautar sabuwar mota. Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyi kan kyautar.
Gwamnatin jihar Kano ta bakin majalisar Shura ga gargadi malaman addini kan yin magana dangane da binciken da ake yi kan Sheikh Lawan Shu'aibu Abubakar.
Yayin da ake cigaba da maganganu kan zargin Sheikh Abubakar Shu'aib Lawan Triumph, an shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi adalci da gaskiya kan lamarin.
Sheikh Barista Ishaq Adam Ishaq ya ce majalisar shura bata hana Sheikh Abubakar Lawal Shua'ibu wa'azi a Kano ba kan zargin batanci da aka masa a jihar.
Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya yi kira da a yi adalci kan zargin da aka yi wa Sheikh Lawal Triump a Kano. Ya bukaci gwamnatin Kano ta yi adalci.
Malaman kungiyar Ahlussunnah a bangaren Izala a Kano sun bukaci gwamnatin jihar Kano ta yi karin haske kan shari'ar da aka yi da batun sakin Abduljabbar Kabara.
Shugaban malaman Kano, Sheikh Ibrahim Khalil ya ce mukabala ba za ta kawo karshen rikicin malamai a Kano ba, ya fadi hanyar kawo karshen rikicin da ake a Kano.
Shugaban Izala reshen Kaduna, Sheikh Bala Lau, ya yabawa hukumar tsaro ta farin kaya, DSS kan abin da ke faruwa game da Sheikh Abubakar Shu'aibu Lawan Triumph.
Kwamitin Shura na Kano wanda ya kunshi manyan malamai masu mutunci ya bayyana cewa zai gayyaci masu korafe-korafe da Sheikh Lawal Triumph don gabatar da hujjoji.
Malaman Izala da darika
Samu kari