Malaman Izala da darika
'Yan Najeriya sun yi Allah wadai da kisan da aka yi wa masu sallar tarawihi a masallaci jihar Kebbi. Bashir Ahmad ya yi Allah wadai da hari a masallacin.
Wata tawagar yan Majalisar wakilai da suka damu da halin da Najeriya ke ciki sun roki malaman musulunci a fadin Najeriya su dage da Al-Qunut a watan Ramadan.
Yayin da ake tsaka da azumin watan Ramadan, 'yan bindiga sun saka wa malamai harajin yin wa'azi a jihar Kebbi. Suna so a biya su N100m kafin yin wa'azi a Utouno.
Malamin addinin Musulunci a duniya, Dr Zakir Naik ya yi kira ga al'ummar Musulmi su dage da ayyukan alheri a Ramadan. Ya fadi abubuwa 25 da ya kamata Musulmi ya yi.
Kungiyar Izala a jihar Kaduna ta kira taron gaggawa a Zaria da Sabon Garin Zaria tare da kira a dakatar da tafsiri saboda rikicin masallaci da ya taso.
Malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi bayani game da karya azumi saboda tsananin wahala. Ya fadi me ake nufi da tsananin wahala a shari'a.
Manyan malaman Najeriya za su gabatar da tafsirin Al-Kur'ani mai girma a jihohi da dama na Najeriya. Mun kawo wurare da jihohin da malamai za su yi tafsiri a 2026.
Ana bukatar kowane Musulmi ya yi shiri na musamman yayin fara azumin watan Ramadan na 2026 domin samun damar yin ibada yadda ya kamata da samun lada sosai a azumi.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ta hannun kungiyar JNI ya fara kokarin tsaftace yanayin tafsirin Alkur'ani a watan Ramadan.
Malaman Izala da darika
Samu kari