
Mawakan Najeriya







Mawaki Abdul Respect ya angwance da Hassana Abubakar a Kano. Shahararrun mawaka da jarumai kamar Ado Gwanja, Momee Gombe, da Ali Nuhu sun halarci bikin.

Mawaki Rarara ya ziyarci masallacin da yake ginawa a Kahutu tare da ziyarar gidan biredin da ya bude, Mama Bread, wanda ya jawo hankalin al’umma sosai.

DJ AB ya gamu da fushin mabiyansa kan bidiyon haraji, wasu sun ce lokacin sakin bidiyon bai dace ba, yayin da wasu suka zazzage masa tare da yi masa barazana.

Mutuwar El-Mu'az Birniwa ta haddasa ce-ce-ku-ce yayin da mawakan Kannywood suka shirya casu kwanaki biyar kacal bayan rasuwarsa, abin da ya fusata Nasiru Ali Koki.

Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ya fara gina sabon masallaci a Kuduri da ke Sumaila, jihar Kano, bayan ruwa ya rushe masallacin da ke garin.

Mawaki kuma jarumi Adam A Zango ya shirya babban casu. A wani bidiyo da ya wallafa a intanet, an ga daruruwan masoya suna nishadantuwa da wakokin Zango.

Rahotanni sun ce mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya kaddamar da gina masallacin Naira miliyan 350 a mahaifarsa da ke karamar hukumar Danja, jihar Katsina.

Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria ya ba mawaki Dauda Kahutu Rarara shawara bayan mutuwar El-Muaz Birniwa inda ya ce hakan ya kamata ya zama izina gare shi.

Fitaccen mawakin Kannywood, Auta Waziri ya na gayyata daukacin masoyansa zuwa daurin aurensa a ranar Juma'a, 6 ga watan Disambar 2024. Ya saki zafafan hotuna.
Mawakan Najeriya
Samu kari