Hukumar Sojin Najeriya
Mataimakin gwamnan Yobe, Idi Barde Gubana zai jagoranci jami’an gwamnati zuwa jana’izar mutanen 37 da 'yan ta'adda suka kashe a Yobe. Sojoji suka kwaso gawarwakin.
A cikin wani bidiyo da aka wallafa, an gano dan ta'adda Bello Turji da yaransa suna shewa bayan samun iko da motocin sulke na sojoji guda biyu a daji.
Gwamnatin jihar Neja ta fara tuntiɓar rundunar sojojin Najeriya domin duba yiwuwar sake buɗe sansanin sojoji a Alawa biyo bayan harin da aka kai kwanan nan.
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin rundunar MNJTF sun samu nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargin su ke safarar miyagun kwayoyi ga Boko Haram da ISWAP.
Hedkwatar tsaro ta ƙasa ta bayyana cewa sojoji sun yi nasrar hallaka ƴan ta'adda sama da 1000, sun kama wasu 1,096, sannan sun ceto ɗaruruwan mutane.
Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalam Abubakar ya ba sojojin Najeriya muhimmiyar shawara kan ba mata damar shiga aikin soja a Najeriya domin inganta aikin.
Hafsan sojojin Najeriya, Laftanar janar Taoreed Lagbaja ya kwantarwa al'umma hankulansu game rashin tsaro inda ya ce saura kiris a gama da matsalar.
Wata babbarkotun tarayya mai zama a Abuja ta amince da bukatar hukumar leƙen asiri ta ƙasa DIA ta tsare mutum 20 da ake zargi da hannu a al'amuran ta'adanci.
A ci gaba da lallashin ƙasashen Nijar Mali da Burkina Faso, babban hafsan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa ya kai ziyara ga takawaransa na Nijar.
Hukumar Sojin Najeriya
Samu kari