Hukumar Sojin Najeriya
Dakarun rundunar soji ta Operation Fansan Yamma sun dakile hare-haren yan bindiga daban-daban a yankin karamar hukumar Kaura Namoda da ke jihar Zamfara.
Rahotanni sun nuna cewa mazauna yankin a karamar hukumar Borgu ta jihar Neja sun shiga tashin hankali bayan bam ya hallaka wasu sojoji da ke ba su tsaro.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya lashi takobin amfani da sababbin fasahohi na zamani wajen yakar duk wata barazana ta tsaro da dawo da zaman lafiya.
Rahotannin da muke samu sun tabbatar da cewa wasu ƴan bindiga sun kai wani hari wata unguwa da ke kan iyakar Abuja da Nasarawa da tsakar daren ranar Juma'a.
Hedkwatar rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarun Amurka da aka turo aikin hadin gwiwa na nan daram, wadanda aka janye sun kammala aikinsu ne.
Kasar Amurka ta janye yawancin dakarunta daga aikin yaƙi da ta'addanci a Tafkin Chadi, amma za ta ci gaba da musayar bayanan sirri da Najeriya a gaba.
Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta ce sojoji sun kashe 'yan ta'adda 1,597, sun ceto mutum 1,516 da aka sace tare da gudanar da ayyukan tsaro sama da 14,000.
Wani da ake zargin ɗan kungiyar ISWAP ne da aka horar tukin kwale-kwalen yaƙi da amfani da bindigar Dushka ya miƙa wuya ga sojoji a Damasak, Borno.
A labarin nan, za a ji cewa dakarun sojin Najeriya sun karbi wasu manyan yan ta'addan ISWAP da suka hana mazauna jihar Borno da kewaye zaman lafiya.
Hukumar Sojin Najeriya
Samu kari