Hukumar Sojin Najeriya
Babbat hedkwatar rundunar sojin Najeriya watau DHQ ta bayyana ainihin abinda ya faru a lokacin da ƴan ta'adda suka farmaki sansanin sojoji a jihar Borno.
Rundunar soji ta 6 da ke sansani a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas ta yi nasarar muƙushe wasu hatsabiban ƴan bindiga da suka kashe sojoji huɗu.
Shugaba Bola Tinubu ya amince da alawus na ritaya ga shugabannin soja, ciki har da neman lafiya a waje, motoci da hadiman gida. Kungiyoyin likitoci sun nuna adawa.
ISWAP ta kai hari kan sansanin soja a Damboa, ta kashe sojoji shida, ta banka wa sansanin wuta. Rikicin na tun 2009 ya halaka mutane 40,000 da raba miliyan biyu.
Jami’an tsaro sun kashe Sani Rusu, ɗan ta’addar Fulani a Tsafe a yayin wani samame, tare da ƙoƙarin kamo abokinsa, dillalin ƙwayoyi, Shamsu Danmali.
NAF ta kai hare-haren sama a Neja, ta kashe shugabannin JAS, ta lalata makamai, lamarin da aka ce ya tilasta mahara guduwa zuwa Birnin Gwari, Jihar Kaduna.
Hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce dakarun soji sun maida hankali wajen tabbatar da tsaron kasa ta hanyar murkushe miyagu.
Gwamma Nasir Idris Kauran Gwandu ya yi ikirarin cewa ƴan bindiga ba su da sansani ko guda ɗaya a jihar Kebbi, daga wasu jihohin makota suke shigowa.
Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayyana kasurgumin ɗan bindigar dajin nan, Bello Turji ya kai hari wani kauye tun kafin wa'adin da ya gindaya ya cika a jihar Sakkwato.
Hukumar Sojin Najeriya
Samu kari