NLC
Gwamnatin Ebonyi ta yi alkawarin fara biyan ma'aikata sabon mafi karancin albashi na N70,000 a watan Satumba. Gwamnatin ta ce tana jira a kammala hada rahoto.
Gwamnatin jihar Kogi karƙashin jagorancin Ahmed Usman Ododo ta kafa kwamitim zai jagoranci yadda za a fata biyan ma'aikata sabon albashi mafi ƙaranci.
Ana zargin DSS da cin zarafin al'ummar Najeriya ba bisa ka'ida ba wanda ya zama ruwan dare kama daga mamayar ofishin SERAP zuwa cafke shugaban NLC, Joe Ajaero.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa aiki ya yi nisa kan batun tsara taswirar da za a bi wajen biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 a Najeriya.
Shugaban kungiyar NLC a Edo, Odion Olaye ya sake rura wutar rikici yayin da ake shirin gudanar da zaben jihar a ranar 21 ga watan Satumbar 2024 da muke ciki.
Kungiyoyin kwadago na duniya karkashin inuwar International Trade Union Conference da Public Service International sun fusata da gwamnatin Najeriya.
Kungiyar kwadago ta bayyana cewa za ta kai shugabanta, Joe Ajaero asibiti domin tabbatar da lafiyarsa bayan kamun da DSS ta masa. NLC ta bukaci a saki takardunsa.
Gwamnatin tarayya ta fito ta yi magana kan dalilin da ya sanya jami'an tsaro suka cafke shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Kwamared Joe Ajaero.
Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gama shiri, tana jiran taswirar aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 ne.
NLC
Samu kari