Labaran tattalin arzikin Najeriya
Ministan noma Abubakar Kyari ya ce Najeriya na samun ci gaba a tsaron abinci yayin da farashin kayan masarufi ke sauka sakamakon shirye-shiryen gwamnati.
Hukumar jiragen kasa ta Najeriya, NRC ta ce za ta kaddamar da taswirar jiragen kasa da za ta ba kowace jihar damar amfana da layin dogo a Najeriya.
Majalisar dattawa ta yi karatu na biyu ga kudirin neman fara aiki da motoci masu aiki da wutar lantarki. Sanatoci sun ce ba za a bar Najeriya a baya ba.
Tinubu ya nemi majalisar tarayya ta amince ya karbo sabon bashin ₦1.15trn don rage gibin kasafin kuɗi, mako guda bayan amincewa da bashin waje na $2.847bn.
Saukar farashin kayan abinci a kasuwannin Najeriya ya kawo farin ciki a tsakanin 'yan Najeriya. Iyalai da dama sun nuna farin ciki tare da fatan hakan ya dore.
Shugaban jami'ar ASE da ke Abuja, Farfesa Mahfouz Adedimeji ya yi kira ga matasa da su yaki talauci, Ya lissafa hanyoyin da za a bi wajen kawar da talauci.
Gwamnatin jihar Borno ta fara amfani da kamfanin hada rabobi da da kayan sola da ake yi a jihar zuwa jihohi. A lokacin Muhammadu Buhari aka kaddamar da cibiyar.
Gwamnatin Bola Tinubu ta kaddamar da sabon tsarin haraji da zai fara aiki 1 ga Janairu 2026, don rage wa matasa da kananan ‘yan kasuwa nauyi wajen biyan haraji.
Alhaji Aliko Dangote ya bayyana dalilin kin sayen matataun man Najeriya. Ya ce akwai kungiyoyi da masu kudi da ya kamata su saye matatun NNPLC a Najeriya.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari