Labaran tattalin arzikin Najeriya
Sanarwa ta nuna cewa Matatar Dangote ta fara sayar da hannun jari 4.1bn kan N525, inda ake sa ran tara N2.15trn domin faɗaɗa ayyuka da ƙarin zuba jari.
Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da shirin Atiku Abubakar na dawo da tallafin man fetur, tana mai cewa zai lalata gyare-gyaren tattalin arziƙi a kasar.
Sarkin Zazzau Ahmad Nuhu Bamalli ya bayyana cewa bai taba tara isasshen kuɗin da zai wajabta masa fitar da zakka ba, yana mai fifita hidima da adalci.
’Yan Najeriya sun yi asarar kuɗi masu tarin yawa a PXES bayan tsarin saka jari ya daina biyan riba, yayin da wasu suka kai hari ofisoshinsa a Adamawa da Kogi.
Kamfanin Dangote yana fatan samun masu hannun jari miliyan 10 a fadin Afirka ta hanyar sayar da hannun jarin matatarsa ta IPO domin ba kowa damar cin moriyar tsarin
Aliko Dangote ya ce hannayen jarin matatar Dangote da ake sayarwa kan N525 na iya kaiwa N10,000, yayin da kananan masu zuba jari za su samu fifiko.
Rundunar yan sanda sun cafke wata Hafsat Abubakar kan zargin ƙirƙira da yaɗa labarin ƙarya cewa OPay zai daina aiki, yayin da bincike ke ci gaba.
Alhaji Aliko Dangote ta fitar da cikakken jerin bankuna, kamfanonin fintech da sauran hanyoyi 32 da aka amince da su don sayen hannun jarin matatar.
Aliko Dangote ya bayyana cewa matatar mansa za ta zama mafi girma a duniya kafin shekara ta 2028 yayin da ake shirin siyar da hannun jarin kamfanin ga jama'a.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari