Labaran tattalin arzikin Najeriya
Shugaban kwamitin gyaran dokar haraji ta gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce kamfanoni 149 ba za su fara biyan haraji ba idan an shiga 2026.
Kungiyar dillalan man fetur IPMAN ta ce farashin mai zai sauka a Najeriya bayan kulla yarjejeniya da matatar Aliko Dangote. Ta ce za ta rika sayen mai wajen Dangote.
Bankin Duniya na shirin amincewa da rancen $500m ga Najeriya domin bunkasa damar samun kudi ga kananan kamfanoni, tare da jawo jarin masu zaman kansu.
Dan majalisar wakilai daga jihar Sokoto, Abdussamad Dasuki, ya yi zargin cewa an sauya wasu sassa na dokokin haraji bayan Majalisa ta amince da su.
Shugaban karamar hukumar Coker-Aguda, Azeez Ogidan, ya gabatar da kasafin kudin 2026 na sama da N11bn domin bunkasa lafiya, ilimi, tituna da jin dadin al’umma.
Ministan kudi Wale Edun ya ce gwamnatin tarayya ta cimma ₦10.7trn kacal wanda ya saba da maganar Shugaba Bola Tinubu da ya yi a Abuja yayin taro.
Kamfanonin rarraba wutar lantarki sun fara rage adadin wutar da suke ba jama'a saboda karancin wutar da ake samar musu. Matsalar ta faro ne saboda karancin gas.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya musamman talakawa cewa sababbin dokokin haraji za su amfani marasa karfi, masu ƙaramin albashi da ’yan kasuwa.
Babban bankin Najeriya watau CBN ya karbe lasisin da ya bai wa wasu bankuna biyu na ajiya da rance, Aso Savings and Loans Plc da Union Homes Savings and Loans Plc
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari