
Hukumar NDLEA







Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta gargadi jama'a a kan sabuwar alewa da aka sarrafa da tabar wiwi, kuma ana sayar da ita ga matasa.

Jami’an NDLEA sun kama dan kasuwa, Chijioke Igbokwe da hodar Iblis 81 a cikinsa. An yi masa tiyata bayan da ƙwayoyi 57 sun makale masa bayan kwanaki bakwai.

Hukumar NDLEA ta kama wani Malam Sabo da ke noma tabar wiwi a jihar Kano. A cikin wani bidiyo, dattijon ya fadi yadda jami'ai suka kama shi a cikin gonarsa.

Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), sun samu nasara kan wasu mutane biyu da ake zargi. Kafin cafke su sai da aka ba hammata iska.

An kama wasu mutane da dama a jihar Kano, Legas, Rivers da Kwara, inda aka kame wani fitaccen dan fim da wasu mutanen da ba a yi tsammani ba a kamen.

NDLEA Kano ta kama mutane 1,345 da kwace 8.4kg na kwayoyi. Ta rushe sansanonin kwayoyi 20, ta gyara halin masu shaye shaye 101 da kuma hukunta 128.

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ta cafke wani dan kasuwa dauke da hodar iblis mai yawa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta samu nasarar cafke wani dan kasuwa daga Brazil wanda ya shigo da hodar iblis zuwa Najeriya.

Wasu 'yan bindiga sun yi aikin bazata a jihar Delta. Tsagerun sun sace wani babban jami'in hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA).
Hukumar NDLEA
Samu kari