Hukumar yan sandan NAjeriya
Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta musanta batun kai hari a makarantar Government Girls College. Sun bukaci jama'a su yi watsi da labarin kai harin.
Shugaba Bola Tinubu ya umarci a janye dukkan ‘yan sanda da ke rakiyar manyan kasa nan take, a mayar da su kan aikin tsaro a yankunan da ke fama da karancin jami’ai.
Masu garkuwa da mutane sun kai hari a Toro, Bauchi, inda suka kashe dan agajin Izalah, Alhaji Muhammad Bakoshi, sannan suka sace matarsa da ‘yarsa mai shekara biyar.
Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya yi tsokaci kan matsalar rashin tsaro. Ya yi bayani kan rawar sa masu bada bayanai ke takawa wajen kai hare-hare.
Rundunar ‘yan sanda ta Gombe ta karyata rahoton harin coci da sace mutane da ya yadu a kafofin sadarwa, tana cewa jami’ai sun kasance wurin tun da safe.
Gwamnatin jihar Kebbi karkashin jagorancin Gwamna Nasir Idris ta yi wa Sanata Garba Maidoki martani. Ta zarge shi shi da yada bayanan karya kan rashin tsaro.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun yi wa jami'an 'yan sanda kwanton bauna a jihar Bauchi. 'Yan bindigan sun hallaka wasu daga cikin jami'an 'yan sandan.
Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta gargadi masu shirya zanga zanga kan sace dalibai a GGCSS Maga a jihar Kebbi. Ta ce hakan zai dagula kokarin ceto daliban.
‘Yan sanda a Kwara sun karyata bidiyon kama wadanda suka kai hari a cocin Eruku, sun ce labarin karya ne kuma ana ci gaba da aikin ceto wadanda aka yi garkuwa da su.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari