Hukumar yan sandan NAjeriya
'Yan ta'adda dauke da bindigu sun yi shigar mata inda suka sace mutane masu yawa a jihar Katsina. 'Yan ta'addan sanye da hijabai sun kai harin ne a Safana.
Rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta cafke wani mahaifi saboda daure dansa da ya yi kan hana shi zuwa wajen kakarsa bayan mutuwar aure da mahaifiyar yaron.
Rundunar yan sanda a jihar Jigawa tabbatar da kifewar kwale kwale a karamar hukumar Auyo inda hadarin ya ritsa da yan kasuwa 20, an ceto mutum 18, daya ta rasu.
Wasu miyagun 'yan bindiga su kai harin kwanton bauna kan jami'an tsaro na 'yan banga a jihar Imo. 'Yan bindigan sun hallaka mutum hudu ciko har da wani yaro.
Wasu makiyaya sun gwabza fada da jami'an tsaro na rundunar Amotekun a jihar Ondo. Makiyayan sun farmaki jami'an tsaron ne kan hana su yin barna a gonaki.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki rundunar 'yan sandan Najeriya kan cin zarafin 'yan Najeriya da kin bin umarnin kotu da take hakkin jama'a.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun bi cikin dare sun sace wasu 'yan jarida guda biyu a jihar Kaduna. Miyagun sun sace mutanen ne tare da matansu da 'ya'yansu.
Rundunar 'yan sandan jihar Delta ta ce jami'anta sun samu nasarar hallaka wani mai garkuwa da mutane a jihar. 'Yan sandan sun kuma cafke takwarorinsa guda uku.
Rundunar yan sanda ta kama wani mahaifi da ya daure dansa mai shekaru biyar da hana shi abinci a jihar Bauchi. Uban ya ce yaron ya addabesu da sata.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari