Hukumar yan sandan NAjeriya
Rundunar yan sanda ta tabbatar da mutuwar wani sufetan dan sanda bayan kazamin harin yan bindiga a jihar Rivers da yammacin ranar Alhamis 7 ga watan Nuwambar 2024.
IGP Kayode Egbetokun ya sanar da tura jami'ai 22,239 zuwa Ondo don tabbatar da tsaro a zaben gwamna mai zuwa. Ya kuma zargi jam'iyyun siyasa da haddasa husuma.
Miyagun 'yan ta'adda sun yi ta'asi a jihar Neja bayan sun hallaka mutane takwas a wani hari da suka kai. Daga cikin mutanen da aka kashe har da wasu mata.
'Yan bindiga sun addabi mutanen wasu kauyukan jihar Zamfara. Miyagun 'yan bindiga sun yanka haraji ga kauyukan wanda ya fara daga miliyoyin Naira.
Rundunar yan sanda ta tabbatar da samuwar yan ta'addar Lakurawa a jihar Sokoto. Miyagu Lakurawa suna da tarin makamai kuma suna da alaka da addini.
Wasu daga cikin yaran da aka tsare saboda zargin shiga zanga-zangar #EndBadGovernance, sun bayyana irin bakar azabar da suka tsinci kansu a ciki.
Yan sanda sun yi nasarar hallaka yan bindiga da suka fitini mutane a jihar Delta. Yan sanda sun kashe yan bindigar ne bayan sun gwabza faɗa da musayar wuta.
Wasu 'yan kungiyar asiri na ci gaba da yakar juna a birnin Makurdi, babban birnin jihar Benue. Fadan ya jawo an samu asarar rayukan mutane tare da dukiyoyi.
Rundunar ƴan sanda reshen jihar Imo ta tabbatar da fashewar bom a kasuwar Orlu ta ƙasa da ƙasa da ke jihar Imo, ta ce miyagu 2 da suka dasa shi sun mutu.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari