Hukumar yan sandan NAjeriya
Rundunar 'yan sanda a jihar Niger ta tabbatar da kama wasu mutane 11 da ake zargi da hannu a saka wutar a sakatariyar karamar hukumar Tafa a jihar.
Tsohon ministan wasanni da matasa, Solomon Dalung, ya fito zanga-zangar da aka fara yi a fadin kasar nan kan tsadar rayuwa da wahalar da ake sha a kasa.
Gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar hana fita har na tsawon awanni 24 domin dakile barnar da ake yi yayin da ake cigaba da zanga-zanga a fadin jihar.
Jami’an ‘yan sandan kasar nan sun tarwatsa daruruwan masu zanga-zanga da borkonon tsohuwa a filin Eagle da ke babban birnin tarayya Abuja yayin da ake su sauya wuri.
Rundunar yan sanda a jihar Kaduna sun yi yunkurin bude kwanar Gwargaje da matasa masu zanga zanga suka toshe. Yan sanda sun fesa borkonon tsohuwa ga matasan.
Wasu daga cikin mutanen da suka fito zanga-zanga sun rasu ransu bayan an bindige su har lahira a Neja. Lamarin ya auku ne yayin da matasa suka fito kan tituna.
Rahotanni sun bayyana cewa daruruwan masu zanga-zanga sun haddasa cunkoson ababen hawa a hanyar Abuja zuwa Kaduna bayan toshe titi a Suleja da ke jihar Neja.
Wani jami'in tsaro ya yi harbi bisa kuskure lokacin da ake gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwar da ake fama da ita a jihar Borno.
Babban sufeton 'yan sandan kasa, Olukayode Ogbetokun ya ce bayanan sirri sun tabbatar da cewa wasu tsageru sun shirya tayar da hargitsi a kasar nan.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari